Babban Bankin Najeriya ya sanar da wasu jerin matakai da ya dauka bayan bullar annobar coornavirus.
Matakan sun hada da
- Bai wa masu kanana da matsakaitan sana'o'i dala miliyan 135 da suka hada da otel-otel da kamfanonin jiragen sama da kamfanonin sarrafa magunguna.
- Bayar da bashi ga kamfanonin hada magunguna da suke da niyyar fadada ko bude kamfanoninsu a Najeriya, da kuma masu niyyar bude asibitoci.
- Sannan da rage kudin ruwa kan basussukan da ke da alaka da shi daga kashi 9 cikin 100 zuwa kashi 5 cikin 100
- Da dakatarwar wucin-gadi kan biyan bankin basussukan da yake bi.

Copyright: Getty Images